1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Sabuwar dokar kula da baki a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
January 14, 2025

Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta gabatar da sabuwar dokar da ta shafi zaman baki tsakanin mutanen kasar, domin sanin yadda baki suke zama tsakanin al'umar kasar da ke yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4p8Xf
Birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
Birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Wannan sabuwar doka wadda shugaban kasar na mulkin soja Birgediya Janar Abdourahamane Tiani ya sanya wa hannu, ta tanadi hukunci mai tsanani kan duk wani bako da ya saba wa sharudan shiga ko zama na baki a kasar ta Nijar. Hakan na daga cikin matakai na dakile duk wani kutse daga masu mugunyar aniya ga kasar ta Nijar.

Karin Bayani: Hare-hare kan motocin dakon kaya a Nijar

Masu zanga-zanga a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
Masu zanga-zanga a birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Wannan sabuwar doka da shugaban kasar na Nijar Birgediya Janar Abdourahamane Tiani ya sa wa hannu, ta ce duk wanda ya taimaka da shigowar wani bako, ko ya saukaka masa zirga-zirgar cikin kasa ko garin da yake ba tare da an bi ka'ida ta shigowa cikin kasar ba, to hukunci zai hau su su duka, kuma ana iya korar duk wanda aka kama ya shigo ba tare da ka'idojin doka ba, sannan idan ya ki mutunta wa'adin korarsa ko ya nemi sake dawowa ta wata barauniyar hanya, an tanadi dauri na shekaru biyu zuwa biyar da tara ta kudi daga miliyan biyar zuwa hamsin, sannan su kuma baki da ke zaume a nan Nijar da su kasance cikin ka'ida a zamansu na kasa daidai da wannan sabuwar doka.

A kasashe da dama dai da suka ci gaba, duk wani mai bulaguro ya san cewa akwai matakai na sanin wanda ya shigo cikin kasa, ina zai zauna sannan me zai yi, wanda a cewar Mamane Bachar, mai sharhi kan harkokin siyasa, dokoki da ma zamantakewa, kuma shugaban kungiyar farar hula ta Reseau Esperance, ya ce mataki ne na zaburar da 'yan kasar domin taka tsantsan kan batun da ya shafi tsaron kasa.

Sojoji a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
Sojoji a birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Da yake magana dan jarida na kasa da kasa, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro da ma zamantakewa Seidik Abba, ya yaba wannan mataki, wanda ya ce akasari masu tafka ta'asa na fitowa ne daga waje su shigo su yi yan kwanaki suna shirya mugun aikin da za aiwatar, sai dai ya ce ya gano cewa dokar za ta haifar da cikas a wani fanni. Tuni dai masu lura da al'amuran yau da kullum ke ganinn cewa, lokaci fa ya yi da ita kanta gwamnati za ta dauki kwararan matakai na mayar da abubuwa da dama na zamani kaman katin dan kasa, lambobin gidaje da ma cikokkun suyayen sabin unguwanni da ma tituna, ta yadda za a samu cikekken adreshi na kowa wanda ake ganin hakan zai sa mutane da dama su shiga taitaiyinsu.