Kura ta fara lafawa a Burkina Faso
September 18, 2015Da alama kura ta fara lafawa a Burkina Faso bayan da sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar a ranar Larabar da ta gabata. Sojin dai sun amince da hawa teburin sulhu da nufin kawo daidaito kan rikita-rikitar siyasar da kasar ke fama da ita. Tuni aka saki shugaban gwamnatin rikon kwarya Michel Kafando.
Shugaban gwamnatin sojan Burkina Faso din Janar Gilbert Diendere ya ce suna kokarin daidaita lamura a kasar, wannan ne ma inji shi ya sanya suka dukufa wajen lalubo bakin zaren warware abubuwan da suka yi wa harkokin cigaba a kasar tarnaki. Janar Diendere ya ce ''mun zanta da wasu jiga-jigan ma'aikatan gwamnati daban-daban don ganin yadda zamu tabbatar cewa ma'aikatun sun na aiki ba tare da matsalaba."
To sai dai duk da wannan, wasu 'yan kasar da suka zanta da manema labarai na cewar ba za su amince gwamnatin da ta yi juyin mulki ta cigaba da jagoranci ba har ma guda daga cikinsu da ya zabi a boye sunansa ya ce ''ba ma son sojoji su rike madafun iko a wannan kasar. Za mu cigaba da yin gwagwarmaya har sai mun ga abinda zai turewa buzu nadi.
Shugabannin Afirka musamman ma na Senegal Macky Sal da takwaransa na Benin Boni Yayi na ta kokari wajen ganin lamura sun daidai a kasar da nufin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar.