Malamai sun kaurace wa azuzuwa a Jamhuriyar Nijar
January 31, 2022Kungiyoyin malaman da suka hada da 'yan kwataragi da masu aikin dindindin sun tsunduma cikin wannan yajin aiki ne, bayan da zaman tattaunawar da suka yi da kwamitin ministocin da ke kula da harkokin ilimi a kasar Nijar ya watse ba tare da cimma matsaya ba, kan jerin bukatun malaman da ke a gaban gwamnati. Malam Mounkaila Halidou, memba a kawancen kungiyoyin malaman makarantun da ya shiga yajin aiki, ya ce jerin koke-kokensu sun hada da bukatar samun albashi a kan kari da kuma samu alawus da suke bin gwamnati.
Kusann illahirin 'yan kwataragi wadanda sune kaso 80% na malaman makarantun boko ne suka kaurace wa makarantu, lamarin da ya sanya ba a yi karatu a akasarin makarntun ba. Wannan hali ya haddasa damuwa ga kungiyar iyayen yara 'yan makaranta wacce ta bukaci bangarorin da su gaggauta komawa kan teburin sulhu domin gano bakin zaren warware matsalar, kamar yadda Ibrahim Nalado, magatakardan kungiyar iyayen yara 'yan makaranta ta kasa ya bayyana.
Gwamnatin Nijar na neman shawo kan matsalolin malamai
Da yake tsokaci kan wannan yajin aiki, Ashana Hima da ke zama daraktan kula da ma'aikata a ma'aikatar ilimi ta kasa ya ce suna ci gaba da neman shawo kan wannan matsala cikin sauri. Wannan yajin aiki dai shi ne na farko da kungiyoyin malaman makarantun bokon suka shiga tun bayan soma karatun sabuwar shekara watanni uku da suka gabata.
'Yan kasa sun zura ido su ga yadda gwamnati za ta gaggauta shawo kan wannan matsala musamman ta la'akari da ikirarin da shugaban kasa Bazoum Mohamed yake yi na farfado da martabar ilimi a kasar Nijar.