Chadi: Muhawara kan aika sojoji yankin Sahel
November 26, 2019Sanarwar da gwamnatin Chadi ta yi ta sake tura dakarunta domin tsare kan iyakokin Mali da Nijar da Burkina Faso domin yaki da ta'addanci ta janyo tsokaci a kasar.'Yan kasar ta Chadi dai na tunanin game da irin kudaden da za a kashe domin tabbatar da tsaro a yankin na Sahel, a daidai lokacin da sauran jama'ar kasar tasu ke cikin wahalhalu.
Makwanni biyu kenan da gwamnatin Chadin ta yanke wannan shawara bayan ganawar da Shugaba Idris Dey Itno ya yi da shugaban kasar Faransa da na Nijar da kuma na Mali dabra da taron da aka yi a Paris.
Kasashen na yankin Sahel dai wadanda suka hada da Mali da Nijar da Burkina Faso har ma da Chadi na cikin wani mawuyacin hali na hare-haren da suke fuskanta na 'yan ta'ada. Abdourahamane Djasnabaye shugaban hadin gwiwar jamiyyun da ke da rinjaye ya ce akwai bukatar taimakawa juna tsakanin kasashen:
"Shugaba Deby ya dau shawara mai kyau ya nuna shi dan kishin kasa ne. Ya kamata mu ba da tamu gudunmuwa ta yadda za a iya magance wannan matsala da ta zama gaggara badau a nahiyar Afirka ta yadda za a yaki Boko Haram a da masu jihadi, mu kare da su kwata-kwata. Ba zamu taba samun ci-gaba ba da matsalar tsaro sai mun yi yadda za mu rabu da wannan matsala a yankinmu domin samun ci-gaba".
'Yan kasar Chadi dai da dama na nuna adawa a matakin na Shugaba Deby wanda suke ganin sai gida ta koshi ake bai wa dawa, sakamakon yadda tarin mataloli suka yi wa kasar yawa. Rassou Gague ya rasa 'yan uwansa guda biyu soja a fagen daga wadanda masu jihadi suka kashe:
"Mun yi asara ta matasa da yawa, 'ya'yanmu, kananmu, saboda wasu soji aikinsu su kare kasarsu ba kasar wasu ba. Ko da ma runduna ce ta Majalisar Dinkin Duniya ya kamata a dau mataki ta yadda idan an sam mutuwa a cikin sojin 'ya'yan wadanda suka mutu za a dauki nauyinsu ko a ba su diyya. Babu rana ta Allah da ba za ka ji a gidan rediyo ba an kashe wannan an kashe waccan ko an yanka wannan. Mu ga shi mun gaza kare kanmu har ma mu ce za mu kare wasu, shin kare rayukan wasu ya fi namu ne?"
Kusan ra'ayi ya zo daya dai tsakanin jama'ar na Chadi da ma 'yan adawar da ke ganin daukar matakin, babban kuskure ne kamar yadda Succes Masra jagoran jamiyyar masu rajin kawo sauyi ya bayyana:
"Ba da gudunmuwar kasarmu wajen yaki da ta'addanci ba laifi ba ne, amma ba za yi haka ba ta hanyar sadaukar da 'ya'yanmu wadanda yawancinsu matasa ne wadanda ake kashewar a fagen daga, kuma yin amfani da maganar tsaro a ci gaba da tsayawa a kan mulki wannan wani kuskure ne kana wani tarkon da Deby ke son saka kasarmu"
Tun daga shekara ta 2015 Chadi ta tura sojoji kusan 1400 domin yaki a ta'addanci kana ta tura sojoji dubu biyu a rundunar tsaro ta kasahen Sahel ta G5 wanda a kan haka kasar a Chadi ta kashe makudan kudade sama da biliyan 300 na CFA.