Najeriya: Kasafin kudi mafi girma a 2018
November 7, 2017Kasafin kudin na badi ya samu kari na kashi 16 cikin dari a kan kasafin kudin kasar na wannan shekara ta 2017. Naira Miliyyan Dubu 558 ce dai gwamnatin kasar ta ware da nufin inganta harkokin wuta da tituna da samar da gidaje. Alal misali dai aikin babbar cibiyar samar da wutar lantarki ta kasar da ke Mambila zai samu naira Miliyan Dubu Tara da dari Takwas. Da kuma naira Miliyam Dubu 20 domin inganta harkokin rabon wutar. Sai kuma layin dogo da ke shirin samun kulawa a cikin kasafin na badi wanda zai baiwa ma'aikatar sufurin kasar Naira Miliyan Dubu 263.
A yayin kuma da batun tsaro ya koma kurar baya tare da Naira Miliyan 145 domin manya na ayyuka. Fannin noma da gwamnatin kasar ke fatan zai kara habaka, shi kuma zai samu Naira Miliyan Dubu 118 a yayin kuma da ma'aikatar harkokin ruwa ta tashi da naira Miliyan Dubu 95. A cikin kasafin da shugaban ya ce zai maida hankali ga ginin sabuwar kasa ta Najeriya:
"Idan za ku tuna a jawabi na na kasafin kudin shekarar da muke ciki ta 2017 na yi muku alkawarin sabuwar Najeriyar da za ta kauce daga dogaro da man fetur. Kiddidigar da ke kasa da sabbin dabarunmu sun kai ga cimma wannan buri yanzu, kuma tsohon tsari cikin kasar na kara bacewa yanzu. Dole ne muyi aiki tare domin tabbatar da dorewar wannan sauyi domin gina sabuwar kasa. Kasar da za ta cida kanta, kasar da a karshe za ta iya kai wa ga ganin amfanin albarkatunta, tunda Najeriyar na da hanyoyi daban-daban na bunkasa tattali na arziki.”
An kai ga ginin tattalin arzikin na badi a bisa Dalar Amirka 45 a kowane gangar man fetur, sannan kuma da iya kaiwa ga hakar ganga miliyan 2.3 a kusan ko wace rana. A badin dai daukacin kudi na manyan ayyukan na zaman Naira Triliyan Biyu da miliyan Triliyan Biyu da Miliyan dubu dari Hudu da ashirin da Takwas a yayin kuma da za a kashe Naira Triliyan uku da Miliyan Dubu 494 ga bukatu na yau da na kullum. To sai dai kuma duk da alamu na dogaro har yanzu a harkar man fetur sabon kasafin dai ya fitar da sabon fata na kaucewa dogaro da al'adar sai man fetur.