1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sa'in sa tsakanin gwamnati da 'yan fafutuka

Salissou Boukari AH
December 31, 2021

Hukumomin birnin Yamai babban birnin kasar sun sake hana wani taron gangami da kungiyoyin fararan hulla na Tournons la Page suka shirya yi a karshen mako.

https://p.dw.com/p/451qM
Niger Polizei
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Ana iya cewa yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara, yanayi na kai ruwa rana a tsakanin 'yan kungiyar farar hulla ta Tournons la Page reshen Nijar da kuma bangaran hukumomin birnin Yamai da ke ci gaba da hana wa wadannan kungiyoyi yin jerin gwano na lumana kimanin mako biyu bayan ziyarar wakilin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yancin walwalar kungiyoyi. Kuma a cewar Moudi Moussa shugaban kungiyar reshen birnin Yamai, dole ne fa sai 'yan Nijar sun tashi tsaye idan suna son fidda wa kansu kitse daga wuta. Ita dai wannan zanga-zanga ko jerin gwano na lumana da 'yan kungiyar ta Tournons la Page ke son yi ta shafi kasancewar sojojin kasashen waje a kasar ta Nijar da kuma matsalar cin hanci da rashin hukunta masu laifi. Kuma wata hira da aka yi da shi shugaban kungiyar farara hulla ta MPCR Alhaji Nouhou Arzika ya ce idan ana son cikkaken hadin kai na 'yan kasa, to a yi hukunci ga wadanda suka yi laifi ta yadda kowa zai shaida cewa ana yin adalci. Masu lura da al’amuran kasar ta Nijar dai na ganin cewa hadin kai ne kawai zai fitar da kasar daga duk wasu matsaloli, yayin da wasu suke cewa ai babu hadin kai idan rashin adalci tsakanin 'yan kasa na samun gidin zama.