1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baraka kan samar da mafaka ga bakin haure a kasashen Turai

Abdourahamane Hassane Alexander Göbel
December 26, 2019

Kungiyar Tarrayar Turai ta dade tana fafutukar ganin an girka wani tsari na ba da mafaka, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba sakamakon yadda ke da akwai baraka a kan batun tsakanin wasu kasashen.

https://p.dw.com/p/3VM1x
Symbolbild: Spanische Rettungskräfte bergen Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Merida

 

Duk da samu raguwar masu tsallaka tekun domin shiga nahiyar Turai amma dai a yankin gabashin na Turan nan aka fi samun masu neman mafaka.

Symbolbild: Spanische Rettungskräfte bergen 200 Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Calvo

Misali a Girka a sansanin yin rejista na masu neman mafaka a tsibirin Egee ya cika makil har ya tunbatsa. Sannan sama da mutane dubu 18 suke zaune a sansanin Moria da ke a tsibirin Lesbo a jumula mutane  kusan dubu 41 suke zaune a cikin sanasanin tsibiran. Wannan shi ne ddadin mafi girma a aka samu tun lokacin da aka kula yarjejeniya tsakanin Turkiyya da Kungiyar tarrayar Turai a game a hana bakin hauren shiga Turai tun a shekara ta 2016.

Kasashe kamar su Poland da Hangari da Jamhuriyar Chek da Slovakiya duk ba su amince da tsarin ba na ba da mafaka ba. Wanda ma tuni tsarin ya rushe saboda yadda Turkiyya ta gaza tare bakin hauren wanda ke kokarin shiga Turai daga Turkiyya akasarin wadanda suka fito daga kasashen Larabawa yayin da hukumomin Girka lamarin ya kai musu iya wuya, saanan babu wata matsaya da aka cimma tsakanin kasashen a game da batun rarraba wadanda ke da yancin samun mafakar a cikin kasashen Turan dabam-dabam.

Europa Migration l Seenotrettung im Mittelmeer - "Ocean Viking" im Hafen von Marseille
Hoto: dpa/J. Naue

Minista cikin gida na Jamus, Horst Seehofer  na ba da shawara a kafa wata cibiyar a wajen Turai wacce za ta rika yin rijista ga 'yan ci ranin da bakin haure a kan iyakar nahiyar ta Turai wacce za ta yi nazarin bukatar shigo bakin kana daga baya a rarraba bakin zuwa ga kasashe dabam-dabam.