'Yan sandan Jamus sun tsinci gawar wata matashiya a motarta
May 4, 2024'Yan sandan birnin Regensburg a jihar Bavaria da ke nan Jamus, sun tsinci gawar wata matashiya mai shekaru 19 a cikin motarta da safiyar Asabar din nan, amma babu tabbacin musabbabin mutuwarta.
Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun cafke 'yan IS kan azabtar da Yazidi
Wani ne dai ya ankarar da 'yan sandan cewa akwai wata gawa cikin wata mota da ke wajen ajiye ababen hawa na wani shagon sayar da kaya, amma an fasa gilasan motar, nan da nan suka garzaya kuma suka dauko ta.
Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun kammala binciken gidan tsohuwar 'yar ta'addar nan Daniela Klette
Yanzu haka sun dukufa da bincike don gano abin da ya faru, kafin fitar da rahoto a kai, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihar Bavaria ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA.