An sami raguwar masu neman mafaka a kasashen Turai
January 11, 2025A cewar hukumar bayar da mafaka ta kungiyar EU, hukumar ta yi rajistar mutane sama da miliyan daya ne a kasashen kungiyar EU 27 da Norway da kuma Switzerland.
Mafi akasarin wadanda suka saka bukatar neman mafakar a cewar hukumar sun fito ne daga Siriya da ke da kaso 15 cikin dari sai Afganistan da ke da sama da kaso 8 da Venuzuela da ke biye mata sai kuma kasar Turkiyya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ofishin da ke kula da kaurar jama'a da 'yan gudun hijira da ke Jamus ya bayyana cewar adadin masu neman mafaka a kasar ya ragu da kusan sama kaso 30.
Ragowar sama da mutum dubu 100 ne aka gani a Jamus din idan aka kwatanta da yawan da aka gani a shekarar 2023.
Jamus dai na zama a sahun gaba na kasashen EU da ta fi samun tururuwar yan gudun hijira.
Karin Bayani: 'Yan gudun hijira sun fara komawa Siriya