Guguwar Haiyan ta haddasa mummunar ɓarnar a Philippine da Somaliya
November 14, 2013Talla
Tun a makon jiya ne mahaukaciyar guguwar nan da ake kira da sunnan Haiyan haɗe da iska mai ƙarfin gaske da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ta afka wa wasu yankunan da ke a gaɓar tekun Philipine,inda ta yi kaca-kaca da gidaje tare da tsinke layukan tarho da na wutar lantarki. Guguwar dai ta fi ɓarna a Tacloban inda dubban jama'a suke cikin wani mawuyacin hali. Sannan kuma guguwar ta bazu har yazuwa Somaliya inda a can ma ta yi mummunar ɓarna. Saboda haka ne muka yi muku tanadin rahotannin waɗanda ke a ƙasa jere.